Majalisar dattawa ta Najeriya ta ce tana gudanar da bincike akan zargin da akewa 'yan siyasa suna amfani da shirin N-Power don tallafawa al'umma domin zaben 2019.
Sanata Shehu Sani wanda ya canja sheka daga APC mai mulki zuwa PRP ya shaida wa BBC cewa idan har suka gano shirin N-Power ya koma na siyasa za su bukaci a dakatar da shi.
"Za mu bukaci a tsaida raba wadannan kudi idan har muka gano 'yan siyasa ke rabama magoya bayansu," cewar sa.
Sai dai kuma gwamnatin tarayya ta yi watsi da zargin, inda Barista Ismail Ahmad, babban mai bai wa shugaba Buhari shawara kan shirin tallafa wa al'umma, ya ce wannan kawai wani yunkuri ne na kushewa da cin zarafin shirin.
Ya ce shirin ba ruwan shi da wata jam'iyya, domin kasuwa a ke shiga a zakulo masu kananan sana'oi domin ba su tallafi ba tare nuna bambanci ba.
Ya kuma kara dacewa a shirye suke su je su kare kansu idan har kwamitin bincike da majalisar dattawa ta kafa ya gayyace su domin gurfana a gabansa.
Ya kara dacewa sun samu korafe-korafe daga jama'a da dama cewar ana karkatar da kudaden ana rabawa magoya bayan gwamna a jiohihi da 'yan majalisu da wasu 'yan siyasa maimakon raba wa talakawa da aka bullo da shirin domin su.
Ya ce ba an kafa wannan tallafi ba ne don taimakawa 'yan siyasa, an kafa shi ne domin taimakon talakawa da 'yan kasuwa.
Ya kuma ce rahotannin da suka samu sun bayyana yadda fom da ake raba wa ke fitowa daga jam'iyar siyasa da jami'an gwamnati.
Kuma a kan haka ya ce idan har suka tabbatar da gaskiyar zarge-zargen, to za su bukaci a tsaida raba kudaden tallafin.
Idan za a yi shi kan gaskiya ne to sai dai a ba kowa, mace ko namji ko tsoho ko matashi da ke bukatar taimakon.
Idan ba haka ba ya kasance ba ya da bambanci da abubuwan da suka faru a gwamnatin da ke baya inda wasu suka yi amfani da damar domin azurta kansu da abokansu da 'yan uwansu dakuma iyalansu. in ji shi.
SOURCE FROM BBC HAUSA
No comments:
Post a Comment